Kungiyar Tarayyar Turai Da Hukumar Kula Da Kananan Yara Ta Majalisar Dinkin Duniya Ta Horar Da Iyaye Mata 2,115 A Jihar Kebbi

EU, UNICEF
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

kungiyar tarayyar turai da Hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya ta horar da iyaye mata 2,115 a jihar Kebbi don habbaka kula da lafiyar matan da suka Haihu da jariransu.

An samo matan da suka amfana da shirin su 2,115 ne daga kanan hukumomi 4 dake yankin daga unguwanni 47.

An horar dasu kan yadda ake awo, shayar da nonon uwa zalla da yadda ake karbar allurar rigakafi.

wata uwa Hajiya Saudatu Auwal, wadda take da yara 3 daga unguwar Allele dake karamar hukumar Jega ta yaba da kungiyar kan wannan horo data bata.

Related stories

Leave a Reply