Kungiyar Shugabannin Makarantun Sakandire Reshen Jihar Bauchi Sunyi Taro

Kungiyar shugabannin makarantun sakandire reshen jihar Bauchi dake arewa maso gabashin najeriya ta kirayi mambobinta dasu gujewa bada satar amsa ko ta wace hanya.

Shugabansu na jiha Dakta Dr Musa Mudi Jahun ne ya bayyana hakan a taron da suka gudanar a made the appeal at the General Meeting of the Association held at makarantar General Hassan Usman Katsina Unity College dake Bauchi.

Dr. Mudi Jahun yace ya zama dole yayi kiran saboda yadda yan sakandire suke zana jarabawa da dama haka nan ya kiraye su dasu zama yan kasa na gari.

Haka nan ya bayyana cewa anyi taron na jiha ne don tattaunawa akan wasu matsaloli kan yadda ake tafiyar da makarantun sakandire a jihar.

Haka nan shugaban kungiyar makarantun masu bukata ta musamman Alhaji Yakubu Ibrahim Hamza ya yabawa kungiyar ciyar da makarantu gaba.

Wakilan NECO da JAMB ma sun tofa albarkacin bakinsu a taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *