Kungiyar Ohaneze Ta Yi Kira Ga Yan Kabilar Igbo Dasu Kaucewa Duk Wani Bore Da Za’a Gudanar A Kasar Japan

igbos
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar Ohaneze ta yi kira ga yan kabilar Igbo dake kasar Japan dasu kaucewa duk wani rikici da za’a gudanar akan shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar Mazi Okechukwu Isiguzoro ne ya bayyana hakan inda yace idan suka kuskura suka tayar da wani rikici hakan zai jawo musu asarar rayuka da dukiyoyi a jihohin Arewacin Najeriya 19.

Haka nan ya kara da cewa kungiyar na kiran yan kabilar Igbo da suke kasar Japan dasu yi watsi da duk wani kudiri da suke dashi na tada rigima a kasar Japan don hakan zai jawo a kulle wasu daga cikinsu san nan a dawo da wasu zuwa Najeriya daga kasar ta Japan.

San nan ya kara da cewa kaiwa shugaba Muhammadu Buhari hari a Japan ba cigaba bane illa ya bata musu suna a sasu a cikin sunayen yan ta’adda a idon duniya.

Related stories

Leave a Reply