Kungiyar Manema Labaran Arewacin Najeriya Sun Koka Kan Kashe-Kashen Da Ake A Yankin

By. Babagana Bukar Wakil

Kungiyar manema labarai yan Arewa dake Najeriya wato NMF da suke kare hakkin yankin sun kirayi gwamnati da ta kawo karshen kashe-kashe, garkuwa da mutane da ayyukkan yan bindiga a yankin Arewa.

Sun bayyana hakan ne bayan da suka lura cewa tsaro a yankin na Arewa na kara tabararewa, inda suka fidda bayanin ta bakin shugabansu Dan Agbese mai taken ‘ A Ceto Arewa’. Kungiyar ta taya shugaba Muhammadu Buhari murnar sake lashe zaben karo na biyu.

Kungiyar tace gwamnatin bata yin abubuwan da suka kamata musamman mahimmai guda biyu da suke a kanta kamar kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.
Haka nan ta kara da cewa duk da Arewa na rike da manyan mukamai kan sha’anin tsaro hakan bai canza zani ba, don haka suke kiran shugaban kasar da gwamnonin kasar da su tashi tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *