Kungiyar Likitocin Najeriya Zasu Tsunduma Yajin Aiki Daga Ranar 7 Ga Wata

strike
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar likitoci na kasa suce zasu tsunduma cikin yajin aiki daga ranar 7 ga watan Satumba idan gwamnati bata biya musu alkawuran da ta yi musu ba.

Kungiyar tace gwamnatin batai musu yadda ya dace ba kan kudaden da tayi alkawri zata bawa ma’aikatan lafiya na aiki cikin hatsari wanda ya kamata a biya a farkon watan Satumba na shekarar 2020.

Shugaban kungiyar Dr. Aliyu Sokomba ne ya bayyana hakan a rohon daya fitar a Abuja.

Inda yace a taron yan kungiyar da suka gudanar 2 ga watan satumba sunce sun bada kwana 21 da a biya su kudaden cikin watan nan .

Haka nan sune suna bukatar gwamnatin da biyasu kudaden gurin zama, inshoran lafiya da kuma kudaden da ake biya idan mutum ya rasu a bakin aikin.

A karshe sun yanke tafiya yajin aikin har sai baba ya gani daga ranar litinin 17 ga wan nan watan har sai an biya su hakkokin nasu.

Related stories

Leave a Reply