Kungiyar Kwadago Ta Najeriya Zata Fara Yajin Aiki Ranar 16 Ga Watan October

nlc2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC sun umarci shiyyoyinsu na jihohi dasu shirya tafiya yajin aiki ranar 16 ga watan October idan gwamnatin tarayya ta karya alkawarin yarjejeniyar.

A takardun da suka aika jihohin wanda sakataren kungiyar Mr Emmanuel Ugboaja, ya sa hannu sun bayyana cewa sun bada 15 ga watan october a matsayin rana ta karshe.

Idan zaku iya tunawa kungiyoyin un bayyana cewa sun bada sati biyu bayan sun tattaunawa. Sun kara da cewa baza a samu rayuwa mai dadi ba har sai an samu an tsaida yarjejeniya tsakaninsu da gwamnati na biyan kayyadajjen albashin N30,000.

Related stories

Leave a Reply