kungiyar Kula Da Almajirai Reshen jihar Adamawa Zata Aika Almajirai 500 Makaranta

ADAMAWA
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

kungiyar kula da Almajirai ta Almajiri Child Right Initiative reshen jihar Adamawa zata aika Almajirai 500 makaranta don su samu ilimi a yankunan su.

Sakataren kungiyar na jihar Ismail Buba Chukkol ne ya bayyana hakan a Yola, inda yace kungiyar zata samarda kayan kiwon lafiya, abinci, takalma, kayansawa da kuma kayan bukata na Almajiran.

Haka nan zasu kirkiri wata cibiyar lafiya don taimakawa yara Almajirai dake yankin. kimanin jihohi 13 ne ciki harda Adamawa da kasar Ingila suka sa hannu kan saka jari a kan ilimin mata da Almajiri.

Related stories

Leave a Reply