Kungiyar Gwamnonin Najeriya Sun Bawa Majalisar Kasar Shawarar Dasu Dakata Da Kafa Dokar Maganganun Batanci

NGF
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar gwamnonin Najeriya sun bawa majalisar kasar shawarar dasu dakata da kafa dokar maganganun batanci har sai sunji suji ra’ayin yan Najeriya kan dokar.

Gwamnan jihar Sokoto AminuWaziriTambuwal ne ya bayyana hakan yayin da yake ansa tambayoyi daga manema labarai bayan sun gama taron da suka gudanar a Abuja.

AminuTambuwal, shine mataimakin shugaban kungiyar inda yace gwamnonin na zasu marawa ko wace doka baya da zata kawo karuwar Haraji a gwamnatin tarayya data jihohi. 

Yayin da yake jawabi kan matsayinsu a kan Karin haraji da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar daga kashi 5 zuwa 7.5, Tambuwal ya roki jama’a dasu fahimci gwamnatin tarayya kan lamarin.  

San  nan yayin da yake Magana kan ranar karshe da kungiyar kwadago tabawa gwamnonin zuwa watan Disamba Tambuwal yace da yawa daga cikin jihohin na tattaunawa da kungiyar kwadagon akai.

Related stories

Leave a Reply