Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Kungiyar Bama Initiative for Human Development Ta Dakatar Da Shirin Ta Na Taimakawa Marayu

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Babagana Bukar Wakil and Mohammed Nur Ali, Maiduguri
Kungiyar Bama Initiative for Human Development tana mai bakin cikin bayyana dakatar da shirin ta na taimakawa da kayaki ga marayu da kuma daukan maraya a karamar hukumar Bama bayan umurnin da ta samu daga gwamnatin jiha na dakatar da al’amuran ta na dan lakoci.

Wannan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da aka mikawa gidan radiyo Dandal Kura ta hannun shugaban amintattun kungiyar Muhammad A. Hassan.

Mohammed A. Hassan ya bayyana cewa dakatar da ayyukan nasu ya zo ne kwana daya bayan sun fara tattara bayanai akan marayu dubu 3 a Bama da Banki wadanda suka rasa iyayen su.

Sanarwar tace gwamnatin jihar Borno ta mika takarda dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Baba Kura Abba Jato domin dakatar da shirin.

Kungiyar Bama Initiative kungiya ce wanda tayi rajista da hukumar cigaba mai dorewa da ayyukan agaji na jihar Borno da kuma kungiyar fararen hula na jihar Borno wanda manufar ta shi ne yabawa ayyukan gwamnati karkashin shugabancin gwamna Babagana Zulum.

Sanarwar ta yi kira ga mambobin ta da cewa ta kwantar da hankalin ta ta jira sakamakon tattaunawa da jami’an gwamnati, shugaban amintattun kungiyar yace yana sa ran komai zai daidaita da yardarm Allah.

Leave a Reply