Kungiyan Manoma Ta Nigeriya Ta Roki Gwamnatin Taraiya da Ta Binciki Hukumar NIRSAL.

farmers-at-work-agriculture
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gamayyar kungiyoyin manoma a karkashin kungiyar dukkan Manoman Najeriya ta roki GwamnatinTarayya ta binciki ayyukan Hukumar bayar da bashin bunkasa ayyukan noma ta NIRSAL.

Kungiyar ta yi  wannan rokon ne yayin wata zanga-zangar lumana da ta gudanar a Abuja.

Wani wakili a kungiyar manoma ta AFAN dake jihar Kano, Mallam Buhari Kura ya yi korafin cewa Hukumar NIRSAL wacce ita Babban Bankin Najeriya ya dorewa alhakin rabawa Manoma bashi domin bunkasa ayyukan nomansu, Hukumar ta ki baiwa Manoman bashin.

Ya koka kan cewa’ya’yan kungiyar wadanda sune ya kamata a ce sun ci moriyar shirin bayar da bashin kai tsaye, amma an hana su inda ya bayyana hakan da cewa matsala ce babba da zata kawo koma baya a kokarin kasar nan na bunkasa noma wadataccen abinci.

Yakuma yi kira ga Shugaban Majalisar dokoki ta kasa da kwamitocin ayyukan gona na Majalisar Dattawa da kuma Majalisar wakilai da Hukumomin tsaro da su binciki ayyukan Hukumar sannan ya bukaci Gwamnati da ta canja shugabannin Hukumar baki daya.

Shi kuwa wani wakili a kungiyar Manoman Tumatur, Mallam Shehu Umar yace babu dan kungiyar koda guda daya da ya samu bashin a cikin shekaru ukun da suka gabata.

A domin haka ya yi kira ga Gwamnati da ta canja shugabannin Hukumar domin ta gaza cimma burin kafa ta.

Leave a Reply