
Kotun koli ta bayyana Sanata Hope Uzodimma a matsayin zababben Gwamnan jihar Imo.
Kotun mai wakilaai bakwai ta yanke wannan hukuncin ne a yau, inda ta bayyana cewa Emeka Ihedioha ba shine zababben Gwamnan jihar Imo ba.
Shi dai Sanata Uzodimmaa ya kalubalanci hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke na amincewa da zaben Ihedioha a matsayin gomna jihar Imo.
A watan Nuwamba na shekara ta 2019 ne Kotun daukaka kara ta yi watsi da kararraki uku da aka shigar gabanta wadanda suke kalubalantar zaben Emeka Ihedioha.
Kotun daukaka karar mai wakilai biyar da Jastis Oyebisi Omoyele ke shugabanta, ta kori kararrakin da dan takarar jam’iyar Action Alliaance Uche Nwosu da dan Jam’iyar APC, Hope Uzodinma da na Jam’iyar APGA, Ifeanyi Ararume suka shigar inda suke kalubalantar zaben Ihedioha.
Yayin da alkalan kotun baki dayansu sun yi watsi da karar da Jam’iyar Action Alliance da na APGA suka shigar, shi kuwa na Jam’iyar APC, Alkalai hudu sun ki amince da karar da ya shigar yayin da guda daya ya goyi bayan karar.
