Korea Ta Kirayi Najeriya kan Ta Kawo Karshen Cin Hanci Da Rashawa

By: YABAWA ISMAILA BORNO

Shugaban kungiyar kawancen kasar Najeriya da kasar Korea da mataimakin kakakin majalisar kasar, Lee Ju-yong, sun kirayi najeriya da ta nemi hanyar kawo karshen cin hanci daga cikin gida wanda hakan ne yake hana cigaban kasa.

Mr Lee ya bayyana hakan a Abuja yayin da ya ziyarci cibiyar al’adu ta Korea yayinda ya jagoranci yan majalisar Korea don bikin rantsar da shugaba Muhammadu Buhari inda yace dole Najeriya ta nemi hanyar kawo karshen cin hanci da rashawa.

A kwanakin baya ne dai aka kulle tsohon shugaban kasar Korea Lee Myung Bak a gidan yari shekara 15 sakamakon cin hanci da kuma wadanda suka gajeshi bayan ya bar aiki wato Chun Doo-hwan da Roh Tae-woo.

Ya kara da cewa Najeriya nada rawar da zata taka wajen kawar da makaman kare dangi inda har yau arewa da kudancin Korea na fama da yake-yake tun bayan ballewarsu a shekarar 1950.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *