Kimanin Kayan Tiriliyan 2.3 AKa Kama A Iyakokin Najeriya Cikin Wata 3

border
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Bayan kimanin wata 3 da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarnin rufe iyakokin kasar, gwamnatin tarayyya tace ta kwace kayan da aka shigo dasu na kimanin Naira tiriliyan 2.3sakamakon sintiri da jami’an tsaro suke a iyakokin kasar

Ofishin mai bada shawara kan sha’anin tsaron kasa ne yake kula da wan nan shirin wanda ya hada da jami’an fasa kauri, shige da fice, yansanda da sojoji.

Mai Magana da yawun rundunar iyakokin kasar da hulda da jama’a na hukumar fasakauri Joseph Attah ne ya bayyana kayan da aka kwace wanda suka hada da bindigogi, harsashai, shinkafa, motoci, magunguna, jarkokin man fetur.

Amma a wata hira da akayi da manema labarai, Attah ya bayyana cewa jami’an tsaron hadin gwiwar  wanda suka hada da hukumomi da dama sun samu cigaba mai yawa ya bayyana cewa jami’an tsaron hadin gwiwar na aiki da junansu inda sukace hakan ya kawo cigaba mai yawa.

Related stories

Leave a Reply