
Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, a ranar talata ya bayyana cewa kasashen Afirka 26 sun karbi sinadarin riga kafi na COVID-19 guda miliyan 15 cikin rahoto data tatara a ranar 21 ga watan maris na wannna shekara.
Guterres ya bayyana hakan ne yayin taro da kungiyoyin Afirka na majalisar ta yanar gizo inda ta bayyana fargabar cewa akwai yiyuwar talautattaun kasashe wadanda basu samu riga kafin na COVID-19 sabanin kasashe masu arziki da suke kokarin bada riga kafi ga duk yan kasar su inda ya bayyana hakan yayin neman Karin sinadarin karkashin COVAX na tabbatar da kasashen sun samu daidaiton sinadarin riga kafin wanda ta kuma ce har yanzu ana bukatan kudi dalar amurka biliyan 2 domin cimma burin ta na bayar wa dukkan mafiya bukata riga kafi a karshen shekarar nan.
Har ila yau yayin taron, Guterres ya nemi majalisar data yaye wa kasashen Afirka basussuka da ake binta domin saukaka tattalin arzikin da kalu-bale da jama’a ke fuskanta a yankin.

Daga karshe ya bukaci kungiyoyi kudi na duniya dasu kara zuba jari a kasashe masu cigaba musamman ma a nahiyar Afirka.
