
Kasar Tanzania ta shirya tsaf don kaddamar da sabon jirgin kasa mafi girma da kuma sauki.
Jirgin zai zamo mafi sauri a jiragen da aka taba kaddamarwa a kasar Afrika wanda ke da sauri fiye da 160.
Yayin da yake bayani kan wa nan cigaba mai matukar mahimmanci da aka samu ta fannin jirgin kasa a wajen garin Dar es Salaam, Ministan ayyuka, sifiri, da sadarwa Eng. Isack Kamwele ya bayyana cewa za’a fara gwada sabon jirgin mai aiki da wutar lantarki a wata Yuli.

Zai fara gwadawa daga kilomita 300 daga Dar es Salaam zuwa Morogoro da tashshin jirgi 6 kafin ya fara aiki a wata Disamba.
Ana ganin hanyar jirgin zata kai shekara 40 kafin ayi mata gyara inda gadar jirgin kuma zata kai shekara 100.
Haka nan an kirkiri fiye da ayyuka 26,000 da za’a bawa ma’aikata haka nan za’a sake daukar wasu idan ayyuka suka kankama.
