Kasar Rasha Zata Taimakawa Najeriya Wajen Farfado Da Kamfanin Ajaokuta

russia large
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin tarayya tace zata hada kai da gwamnatin rasha don farfado da Ajaokuta Steel Company.

Ministan ma’adanai da albarkatun kasa Mr Olamilekan Adegbite, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da suka gudanar da kwamintin ma’adanai da albarkatun kasa na majalisar dattawa a Abuja.

Ya bayyana cewa shine makasudin da zaisa shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara kasar Rasha sati mai zuwa don tattauna yadda za’a farfado da kamafnin na Ajaokuta.

Haka nan ya kara da cewa Rasha ta nuna ra’ayinta na taimakawa kasar Najeriya kan farfado da kudinta.

Adegbite yace ba wanda ya lalata kamfanin Ajaokuta kamar yadda wasu suke fada.

San nan ya bayyana cewa wasu gwamnonin jihohi na maraba da wannan tsarin na shigar kasashen waje.

Shugaban kwamitin Sanata Tanko Almakura yace dole a fadakar kuma a karfafawa jihohi da kananan hukumomi gwiwa don kar su shiga ba bisa ka’ida ba.

Related stories

Leave a Reply