‘Kasar Amurka Tayi ‘Kira Ga Gwamanti Najeriya da ta Hukunta Wadanda Suke Haddasa Husumar A Kasar

‘Kasar Amurka ta yi ‘kira da a tsare wadanda suka haddasa tashin-tashinar da ya auku a baya wadda ya lakume rayukan dimbin al’umma a Najeriya.
Mataimakin jakadan ‘kasar Amurka a tarayyar Najeriya Mista David Young, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin ‘kasar Amurta ta rubuta a shafinta na Twitter, wadda ya yi ‘kira da gwamanti da ta hukunta wadanda suke haddasa husumar.
Hari la yau ya ce rikicin da ya wakana a baya ya lakume rayukan jama’a da dama, wadansu kuma sun tsere daga muhallinsu, sa’annan rikicin ya daidaita iyalai da dama sanadiyyar rikicin da ya wakana a jihar Pilato, da kuma tsakanin manoma da makiyaya.
Haka zalika ya ‘kara da cewa gwamantin ‘kasar Amurka da ofishinta na tarayyar Najeriya suna aiki tukuru da ‘kungiyoyi a sassan ‘kasar domin kare fararen hula da kuma martaba hakkin bil adama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *