Kamaru Zata Dawo Da Yan Najeriya 4,000

By: Babagana Bukar Wakil Ngla

Jami’an kasar kamaru na nan na shirin dawo da yan gudun hijirar Najeriya 4,000 zuwa kasar su nan da 29 ga watan Aprilu.

Gwamnan yankin Midjiyawa Bakari ne ya bayyana hakan inda yace yan gudun hijirar dake sansanin Minawao dake arewacin kasar ne zasu dawo gidan.

Bakari ya bayyana wa manema labarai cewa sunyi yarjejeniya da gwamnatin Najeriya cewa zasu dawo da mutane 4,000 wadanda suka je daga jihar Adamawa a jirgin sama.

Kasar Najeriya da kamarun na nan na tattaunawa kan yadda za’a kula da ilimin yaran. Yan Adamawan zasu koma ne yayin da aka samu tsaron a yankinsu.

A farkon watan Aprilu ne kasar kamaru ta taimakawa kimanin yan Najeriya 40,000 cikin 60,000 suka samu suka dawo gida daga kasar ta kamaru.

Sansanin yan gudun hijira na Minawao na dauke da kimanin yan gudun hijirar Najeriya 57,000 wadanda suka gudu saboda rikicin Boko Haram.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *