
Kwamitin da ya shirya taron gama gari na yan a ware ya dage taron zuwa 19 ga watan Nuwamba ba tare da bayyana dalilin hakan ba.
Kwamitin yace yana ta jiran a bashi damar gudanar taron bayan ya mika takardar neman izini, sunce suna kiran kasashen duniya dasu ci gaba da basu hadin kai da taimako.
Za dai a iya tunawa masu shirya taron wanda Emeritus Archbishop yake jagoranta har sun isa Bua a hutun mako don jiran a basu damar wanda har yanzu shiru.
