Jirgin Sojojin Pakistan Ya Fadi A Birnin Rawalpindi

pakistan
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Mutane 18 ne suka rasa rayukan su sakamakon tarwatsewar jirgin soji a birnin Rawalpindi na kasar Pakistani.
Jirgin ya tarwatse ne akan wani kauye kusa da wani babban barikin sojoji, inda wuta ta rika ci ba jib a gani. Wannan kuma, ya matukar razana mazauna kauyen.

Rahotanni sun nuna cewa, an kai gawarwakin mutane 18 zuwa asibiti, 13 daga ciki fararen hula ne sai kuma 5 ma’aikatan jirgin. Sa’annan 12 sun samu rauni a cikin hatsarin kusa da babban birnin kasar Islamabad.

saboda konewar da gawarwakin sukayi, sai likitoci sunyi bincike akan kwayoyin hallitar su. In za a iya tunawa, an samu mummunar hatsarin jirgin sama a tarihin Pakistan a shekarar 2010 a yayin da mutane 152 suka halaka, a yayin da jirgin su ya tashi daga Karachi zuwa Islamabad.

Related stories

Leave a Reply