Jihohi 18 Zasu Amfana Da Shirin Bankin Duniya A Shekarar 2020

Jihohi 18 a najeriya zasu amfana da shirin taimakawa mazauna kauyuka da bankin duniya ya shirya a shekarar 2020.
Mr Ubandoma Ularamu wanda ya shirya shirin ne ya bayyana hakan yayin bude shirin kasha na 2 a Yola dake jihar Adamawa a Arewa maso gabashin Nigeria.

Ularamu yace kashi na 3 na shirin zai kunshi harkar noma wadda zata bunkasa harkar abinci a Najeriya. Ya kara da cewa jihohi 13 da aka zaba duk suna da nasaba da noma kuma an zabe su a yankuna 6 na kasar.

Shugaban shirin ya kirayi yan kwangila da kada su maida abun sana’a don shirin zai samar da ayyuka da dama.
Jihohin da zasu fara amfana sune Kaduna,Cross Rivers, Adamawa, Enugu, Niger, Osun da Imo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *