Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Jami’an Tsaro Sun Rista Yan Kungiyar Boko Haram Masu Karbar Haraji

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojojin Najeriya a yammacin ranar Litinin, 22 ga watan Maris, sun yi kwanton bauna tare da kashe wasu gungun ‘yan kungiyar Boko Haram / ISWAP wadanda rahotanni ke cewa suna kwasar ganima a yankin Magumeri na jihar Borno.

Wannan na zuwa ne yayin da sojoji daga wani bangare suka kashe wasu yan Boko Haram wadanda ke karbar haraji daga Mazauna da makiyaya a yankin Geidam na jihar Yobe.

Majiyoyi sun fadawa manema labarai cewa bayan wani sumamen sirri, sojojin karkashin jagorancin Laftanar Kanal Ibrahim Bunu sun hango ‘yan ta’adda da yawa da misalin karfe 5 na yamma a kan babura kimanin 10 da ke kan hanyar zuwa unguwar Ngowala da ke cikin Karamar Hukumar Magumeri, inda suka yi musu kwantan bauna tare hallaka su.

Sojojin sun kai wan nan sumamen da rakiyar yan kungiyar sa kai na civilian JTF.

Haka nan sun samu manyan makamai daga ‘yan ta’addan wadanda suka hada da bindigogin AK 47, bindigogin Barreta, gurnet din hannu da Sauransu.

Ragowar sune wayoyin hannu, kayayyakin abinci da suka karba daga mazauna garin.
A halin da ake ciki, wasu da ake zargi ‘yan ta’adda ne wadanda ke karbar daga mutanen gari da makiyaya a Geidam, jihar Yobe sun tsere kan ganin sojojin da ke tafe.

‘Yan ta’addan sun kasance suna yin kwace ga mazauna garin da makiyaya a kauyukan Abari, Dawayya, Gonisaleri da Tattukuttu da ke karamar hukumar Geidam.

Wani dan asalin gari ya fadawa Wakilin gidan Rediyon DANDAL Kura Alh Sherif Bura cewa ‘yan ta’adda suna karbar tarar saniya daya a cikin kowane shanu 40 a
matsayin haraji sannan suka ba da rasiti ga makiyayan da suka bayar kafin biya na gaba.

Haka nan Sojojin naci gaba da mamaye wasu yankuna gaba daya da kuma ci gaba da bin ‘yan ta’addan da suka gudu

Leave a Reply