Jami’an Sojojin Sudan Zasu Rike Mulkin Kasar Na Shekara 2 Kafin Ayi Zabe

Shugaban jami’an sojojin Sudan ya tsaya da kafarsa wajen ganin an yiwa shugaban kasar Omar al-Bashir juyin Mulki wanda yan kasar suka dade suna zanga-zanga.

Ministan tsaron kasar Awad Ibn Auf ya bayyana a gidan talabijin a kasar cewa Lt-Gen Abdel Fattah Abdelrahman Burhan ne zai maye gurbin sa.

Jami’an sojin sunce zasu Mulki kasar na shekara biyu kafin a sake gudanar da zabe amma yan kasar masu zanga-zangar sunce baza su bar kan tituna ba har sai sojojin sun bada mulkin ga fararen hula.

Saukar Al-Bashir’ din daga kan Mulki nada nasaba da yawan zanga-zangar da akeyi tun watan Disamba kan hauhawar farashi, manema labarai da suka zanta da mutane a kasar sun tabbatar cewa mutumin da aka ba rikon kwaryar nada kyawawan halaye fiye da ragowar jami’an sojin. Kuma yace zai gana da masu zanga-zangar yaji ta bakinsu.

Kotun masu lafi ta duniya ce dai ta fara kama Al-Bashir din kan rikicin da akayi a Darfur wanda ya haifar da rikici.

Mata yan jarida na Sudan sun kirayi jami’an sojin ta kafar sada zumunta na Facebook dasu bada mulkin ga fafaren hula.

Yan sandan kasar sun bayyana cewa Kimanin mutane 16 suka mutu yayin da bulet ya kubce ya same su yayin zanga-zanga ranar Alhamis da Juma’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *