
Aci gaba da kai hare-hare da jami’an sojojin saman Najeriya sukeyi ga ‘yan kungiyar Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya rundunar ta tarwatsa wata maboyar tasu a dajin Sambisa dake jihar Borno.
Sun gudanar da aikin ne bayan da suka samu bayanan sirri na na’ura wanda ya nuna cewa ‘yan kungiyar sun taru a wani sabon sansani da suka bude cikin dajin kuma sun kakkafa gurare da dama a boye cikin dajin.
Rahoton da mai Magana da yawun rundunar air kwamanda Ibikunle Daramola ya fitar ya bayyana cewa za’a ci gaba da kai hare-haren har sai kawo karshen yan ta’addan a Arewa maso gabas.
