Jami’an Sojojin Najeriya Sun Mayar Da Mutanen Jakana Garinsu

Rundunar sojojin Najeriya sun mayar da mutanen kauyen Jakana dake karamar hukumar Konduga a jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya gidajensu bayan da suka shafe kwanaki uku a sansanin yan gudun hijira na Bakassi dake birnin Maiduguri.

Zamu iya tunawa dai jami’an sojin na Operation Lafiya Dole sun dawo da yan garin sansanin yan gudun hijira dake Maiduguri don a samu a kakkabe yankin nasu ba tare da abun ya shafesu ba.

Yayin da ake gudanar da ayyukan Birgediya Janaral Sunday Ikinom Wanhia ya kirayi mutane da su bawa jami’an nasu hadin kai musamman bada bayanai masu mahimmanci.

Haka nan jami’an sun jaddada cewa zasu yi kokarin ganin sun kakkabe yan ta’addan a yankin gaba daya. San nan ya yabawa mazauna garin kan yada suka zana a sansanin na Bakassi da yadda suka bawa jami’an tsaro hadin kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *