Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Jamhuriyar Ta Hana Bara A Tituna Da Kofar Shaguna

niger map small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumomin kasar Nijar sun hana bara a kan tituna, bakin titi da kofar shaguna a fadin babban birnin kasar na Niamey daga ranar daya ga watan Mayu na shekarar 2019.

Haka nan hukumonin sun hana barar da kananan yara suke yi kwata-kwata inda suka ce manyan kawai za’a iya kyalewa don neman taimako kamar a wuraren ibada da wasu bukukuwa.
Wan nan ya biyo bayan da aka gana da ma’aikata, shugabannin addinai, sarakunan gargajiya da kungiyoyin fararen hula a garin Niamey.

Haka nan an yanke wan nan hukuncin ne sakamakon yawaitar barar a kasar da kuma shirin taron kungiyoyin Afrika da za’ayi nan da wata 3.

Related stories

Leave a Reply