
Jakadan kasar ingila a kasar Amurka Kim Darroch ya aje aikinsa kan wata rigima ta hadin kan kasashen.
Darroch yace lamarin ya zamar masa dole ne saboda baya samun damar gudanar da ayyukansa yadda ya kamata. Sannan ya kushe gwamnatin shugaban Amurkan Donal Trump inda ya kira ta da gwamnatin da bata yin abubuwa yadda ya dace da kuma gwamnatin da bata san me takeyi ba.
Shugaban kasar Donald Trump yayi alla wadai da bayanin Darroch inda yace shi ba abinda zaiyi da jakadan.

