Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

ISWAP Ta Katse Wutar Lantarki A Jamhuriyar Nijar

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

ISWAP sun kaddamar da yakin saka al’ummar jamhuriyar Nijar da Najeriya da sassansu a cikin duhu.
Masu tayar da kayar bayan na kungiyar Islamic State West Africa (ISWAP) a ranar Juma’a, 26 ga Maris, sun yi yunkurin murkushe kokarin gyara layukan wutar da kungiyar ta lalata a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Jamhuriyar Nijar, kusa da kan iyaka da Najeriya.

Kungiyar a safiyar Alhamis, 25 ga Maris, ta lalata layin wutar Mainé-Soroa- Diffa.

Sojojin Nijar dana Kamaru, tare da tallafin na sojin sama sun yi fatali da harin na ranar Juma’a da mayakan ISWAP suka yi a wurin gyaran layin wutar a kan manyan motoci masu dauke da bindiga.
An kashe ‘yan tawayen uku daga baya kuma an kwato kayayyakin sojoji.

A ranar 9 ga Maris, Kamfanin Wutar Lantarki na Nijar (NIGELEC) ya sami damar dawo da layin wutar da ya hada sashen Diffa da Maine-Soroa bayan barnar da maharan suka yi a ranar 7 ga Maris.

Dukkanin ISWAP da Boko Haram dake kewayen Tafkin Chadi suna gudanar da hare-hare a cikin Diffa yankin Jamhuriyar Nijar.

A shekarar 2003, akwai wani rahoto da ya nuna cewa Chetimari da ke Yankin Diffa za a hada shi da garin dake kan iyaka na Najeriya na Damasak da ke Jihar Borno, a karkashin shirin Project for the Development of Niger’s Interconnected Electric Network planning.

Ana sa ran hanyar sadarwar za ta hade garuruwa a yankin na Diffa da suka hada da Maine Soroa, N’Guigmi da Diffa zuwa Damasak a Najeriya.

A Najeriya, kungiyar ISWAP ma ta lalata wutar lantarki dake kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, ‘yan kwanaki kadan bayan da aka maido da wutar

zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno

Leave a Reply