ICRC Tace Najeriya Ta Dauki Rahoton Mutane 24,000 Da Suka Bar Yankunansu

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar bada agaji ta International Committee of the Red Cross (ICRC) tace Najeriya ta dauki rahoton mutane 24,000 da suka bar yankin inda suka ce fiye da rabin mutanen Afrikan sun bar kasar.

Mr Aliyu Dawobe, jami’in huda da jama na kungiyar ne ya fitar da hakan a jiya a Abuja, inda yace fiye da mutane 44,000 ne a Africa akayi rigistar basa kasar ciki hard a yara kashi 25.

Ya kara da cewa kashi 82 da akayi rigistar basa nan a kasashen afrika sun hada da Nigeria, Ethiopia, South Sudan, Somalia, Libya, kamaru da jamhuriyar Congo.

Haka nan yace wadanda basa nan a Afrikan nada matukar yawa a yankin.
Ya kuma ce fiye da kashi 90 rikicin yan bindiga ne musamman a yankin Arewa maso gabas inda kashi 57 yara ne. wasu kuma suma sun bata.

Acewarsa ranar 30 Augusta ce ranar ta tunawa da wadanda suka batan na duniya kuma ICRC da iyalai day an uwan wadanda suka batan suna tunawa da wan nan ranar.
San nan yace ICRC ta tabbatar da cewa suna tare dasu a kullum basu manta dasu.

Dawobe ya kara da cewa nahiyar Afrika sun samu Karin mutane da dama da sukayi wa rigista sakamakon batan da sukayi tun shekarar 2020, saboda rikice-rikice.

Ya kara da cewa annobar COVID-19 da ta afku farkon 2020 tayi sanadiyyar Karin kalubale da dama ga mutanen da suka bata.

Ya kuma ce ICRC zata cigaba da taimakawa yan uwa da iyalan wadanda suka bata.

Leave a Reply