Hukumar Tsaron Amurka Ta Kama Dafe Ejebor da Wasu 46 Kan Safarar Mutane

Hukumar tsaron Amurka ta kama tsohon janaral manaja na hukumar zuba jarin mai Dafe Ejebor da wasu 46 da sa hannunsu cikin safarar mutane ba bisa ka’ida ba.

Bangaren yansanda na Houston da wasu ma’aikatun sun gudanar da taro bayan da aka kama mutane da dama da akayi safarar su bayan wani bincike da suka gudanar.

Wadanda aka kama sun hada da mata 27, maza 20, wasu ma’aikata da suka gana manema labarai sun bayyana laifukan da ake zargin nasu dashi.

Ciki harda kananan yara, da mallakar wasu abubuwa ba bisa ka’ida ba, daukar makamai ba bisa ka’ida ba, karya shaidu da karuwanci..

Sgt. John Wall dansandan hukumar a ya bayyana cewa a kamen da suka yi sun samu kana nan yara 2 wanda karamin da shekara 16 ne.

ya kara da cewa matsalar safarar mutane na shafar wadanda aka kai din kuma suna jin tsoron bayyana kansu amma zamu yi kokarin ganin mun kare su kuma mu nema musu abin da zasu dinga yi don su ci gaba da rayuwarsu.

Haka nan ya jaddada hukunta masu safarar mutanen ko da kaisu gidan yari ne inji Wall.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *