Nigeria: Hukumar Muhalli Ta Abuja Ta Koka Kan Yadda Sai Da Naman Jakuna Ya Zama Ruwan Dare

Abuja
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar muhalli ta Abuja ta koka kan yadda sai da naman jakuna ya zama ruwan dare a babban birnin tarayyar.
Malam Baba Lawan, Daraktan hukumar ne ya fitar da rahoton a Abuja, inda ya koka da yadda ake saida naman mara inganci ga lafiya ga mazauna babban birnin tarayyar.

Lawan ya fitar da rahoton inda Malam Muktar Ibrahim shugaban sashin yada labarai yasa hannu sun bayyana cewa sam baza a yadda da wan nan ba.

Hukumar ta bada umarni da akwace kuma a lalata duk wani danyen nama da aka kama ana sayar wa akan hanya a Abuja.
Ministoci zasu zauna su duba yadda za’a kafa matakan gaggawa kan yadda za’a dinga yanka dabbobi a mayankar dake Abuja inda za’a tabbatar da duk naman da ya fito daga mayankar mai lafiya ne kuma yana da inganci.

Related stories

Leave a Reply