Hukumar Matasa Masu Yiwa Kasa Hidima Tace Shirin Baiwa ‘Yan Rukuni Na Daya Na Matasa Masu Yiwa Kasa Hidima Horo Yana Nan Daram Dabu Canji

nysc
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar matasa masu yiwa kasa hidima ta yi watsi da labaran da ake bazawa ta kafofin sada zumunci cewa ta dage shirin horad da masu yiwa kasa hidima na rukuni na daya na shekara ta 2020 sakamakon tabbatar da bullar cutar Corona virus a Legas.
A sanarwr da Mai magana da yawun Hukumar, Mrs Adenike Adeyemi ta bayar a Abuja, tace Matasan zasu shiga sansanonin horad da sune din kamar yadda aka sanar tun da farko, inda ta kara da cewa an dauki matakai na kariya domin tabbatar da cewa babu wanda zai kamu da cutarr a yayin zamansu a sansanonin.
Mrs. Ta bayyana labaran da ake bayarwa a kafofin sada zumunin da cewaa ba komai ba ne sai kokarin sanya fargaba a zukatan Matasa da zasu yi aikin hidimar kasar.
Hukumar ta tabbatarwa da Jama’ar kasar nan da kuma Matasa da zasu yi aikin hidimar kasar cewa kamar yadda ya faru a lokacin da aka samu barkewar cutar Ebola da ake sanya zazzabi mai tsanani, haka ma a wannan karon Hukumar tana aiki tare da Ma’aikatar lafiya ta Tarayya domin tabbatar da ganin cutar bata bulla a sansanonin ba.
Sanarwar ta jaddada cewa shirin horad da matasa masu yiwa kasa hidimar na ‘yan kuruni na daya na shekara ta 2020 za’a gudanar da shi a fadin kasar nan kamar yadda bayar da sanarwa tunda farko.

Leave a Reply