Hukumar Masu Yiwa Kasa Hidima Ta Ce Baza Ta Biya Kudaden Fansa Na Ko Wane Dan Bautar Kasa Ba

nysc
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar masu yiwa kasa hidima ta ce baza ta biya wasu kudaden fansa na ko wane dan bautar kasa ba da akayi garkuwa dashi ba.

Haka nan sun kirayi yan bautar kasar dasu su dinga kula da guraren dasu je. Darakta janaral na hukumar, birgediya janaral Shuaibu Ibrahim ne ya yayi bayanin inda yace ya kai ziyarar bazata ne gay an bautar kasar dake Katsina na jihar Borno wanda suke karbar horo a can.

Haka nan ya basu shawarar da kar su dinga yin dare a guraren da suka je. Wan nan ziyarar itace karo na biyu da ya kai jihar ta Katsina cikin wan nan satin inda yakai ta farkon bayan mutuwar yan bautar kasar 3 da suka rasu bayan sunyi hatsari.

Related stories

Leave a Reply