Hukumar Kula Da Abinci Da Magunguna Tace Ya Kamata Jama’a Su Tabbatar Da Rigakafin Ta Astrazeneca

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna wato NAFDAC ya bawa yan Najeriya shawarar karbar rigakafin Astrazeneca kan cewa tana da inganci.

Hukumar ta gargadi jama’a das u tabbatar da cewa mutane sun karbi rigakafin ta Astrazeneca ta gaskiya.

Hakan na cikin sakon da babban daraktar hukumar farfesa Mojisola Adeyeye ta fitar a jiya a Abuja.

Adeyeye ta bayyana cewa asalin allurar ta Astrazeneca an samo ta daga jami’ar Oxford daga babban kamfanin India dake sarrafawa duniya magunguna ya sarrafa mai suna Serum Institute of India (SIIPL).

Oxford sun bawa kamfanin na Serum Institute of India sarrafa maganin don siyarwa, wanda shine babba a duniya baki daya wanda suke sayarwa duniya .

Kamfanin ya samar da fiye da biliyan 1.5 wanda suka sarrafa allurar rigakafin shan inna, ciwon hanta, kyanda da sauransu.

Leave a Reply