
Hukumar albarkatun man fetur DPR ta rufe gidajen mai 19 a jihar Niger bayan ta kamasu da sayar da mai sama da farashin lita naira 165 da gamnati ta amince dashi
Hukumar ta rufe gidajen man a jiya bayan gudanar da bincike da conrolan hukumar a Minna, injiniya Abdullahi Isah Jankara ya jagoranta.
Injiniya Jankara ya bayana manema labarai cewa, za’a dauki dukkan mataki don tabbatar da cewa yan kasuwan mai sun sayar a farashi da aka saka, kuma yayi jan kunne ga masu aikata iren-iren hakan da cewa tabbas doka zaiyi aiki a kansu.

Yace, sun gano yan kasuwa dake sayar da litan mai akan naira 175 da 185, sabanin 165 da gwamnati ta tsayar inda yace an rufe gidajen man da aka kama da aikata hakan kuma zasu biya kudin .
Ya kara da cewa an rufe gidajen mai 16 a Kontagora, 2 kuma a Tegina, sai 3 a Minna.
Ya kuma ce zasu ci gaba da tsanantawa har sai yan kasuwan sunyi aiki dai-dai da dokar gwamnati inda ya kuma shawarce sauran yan kasuwan da suyi aikin su karkashin dokar na gwamnati domin gujewa hukunci.
Injiniya Jankara ya dangana dukkan nasarorin aikin ga hukumar a yankin wanda ta tsara dukkan matakan don tabbatar da anyi aiki da doka.
