Hedikwatar Tsaron Najeriya Ta Kafa Kwamitin Tsaro Kan Kisan Yansanda 3 A Taraba

Defence headquaters
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kwamitin da hedikwatan tsaro ta kafa komitin bincikan domin kisan yan sandan nan guda 3 da akayi a Ibi a jihar Taraba, a yanzu haka yabada umarnin ayi bincike a kan tona asirin da mashahurin mai garkuwa da mutanen nan Hamisu Wadume yayi inda ya zargo sojoji a sakinsa da sukayi daga hannun yann sanda.

A cikin wani faifan bidiyo da wadume yayi wannan warwara, yace bayan yan sanda sun kama shi, sai sojoji suka bisu suka bude wuta kuma suka cire ankwan dake hannunsa suka sakeshi a hedikwatan sojoji.

Wata majiya a hedikwatan tsaro tace wannan bankada da wadume yayi ya tada hankalin manyan jami’an sojojin kasan nan a don hakane suka bukaci Karin lokaci domin su kamala aikin da aka basu na wannan bincike.

Kwamitin binciken yana karkashin Rear Admiral Ibikunle Olaiya.

Related stories

Leave a Reply