Za’a Habbaka Noman Kifi A Kasar Najeriya.

nigeria
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ma’aikatar noma da raya karkara na tarayya tare da hadin guiwar Partnership Initiative zasu hada hannu domin habbaka noman kifi a kasar Najeriya.

Daraktan bangaren noman kifi a ma’aikatar Dr. Ime Umoh shi ya bayyana haka a Abuja, yace manufar su shine tabbatar da wadataccen abinci.

Ya bayyana haka a wajen taro karkashin shirin ciyar da kasa wanda kungiyar USAID tare da hadin guiwar PIND suka dauki nauyin ta na shekaru biyar wato daga shekarar 2020 zuwa 2025.

An aiwatar da aikin ne a jihohin Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Kaduna, Kebbi, da kuma Naija wanda Winrock International ta shirya.

Aikin na sama da dala miliyan 16 ya maida hankali ne kan noman masara, shinkafa da waken soya kuma ana sa ran zai sanya kananan manoma akalla miliyan 2 sanin hanyoyin noma na fasaha tsakanan shekarar 2020 zuwa 2025.

Ya kara dacewa yana da muhimmanci a samar da bangaren saboda gudumawar ta ga kasa da al’umma wajen samar da aiki da wadataccen abinci musamman yankunan bakin take da suka hada da Naija Delta.

Daga karshe yace yana da niyyar kara noman kifi domin taimakawa kananan manoma wajen rage yunwa da talauci a kasa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply