Zaa Gina kwalejin Kimiya Da Fasaha A Karamar Hukumar Monguno Dake Jihar Borno.

images (52)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban hukumar jami’o’i da malaman jami’a, Matawalli Kashim Iman yace, gwamnatin tarraya ta kaddamar da ginin kwalejin kimiya da fasaha a karamar hukumar Monguno dake jihar Borno.

Ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci tawagar hukumar ta TETFUND lokacin dasuka kai wa Gwamnan jihar farfesa Babagana Umara Zulum a gidan gwamnatin a babban birnin Maiduguri.
Jihar Borno tana cikin jerin jihohin da batada kwalejin tarraya da kuma kimiya da fasaha ta gwamnatin tarraya a kasar. Wanda kowacce jiha ya kamata tanada duka biyun.
Matawalli yace, ya dauki kudirin aikin a lokacin daya shiga ofis kuma shugaban kasar ya kaddamar da ginin jami’o’i biyu wanda daya yake a jihar Borno.
Manyan shuwagabannin hukumar TETFUND dasuka kai ziyarar sun hada da Tijjani Musa Isa, senata Ganiu Solomon, Dr. Afrevo Clever, Liman Chiroma, da Mrs Roseline Colade mai wakilkar ma’aikatar kudi da sauran su.
Kashim Imam ya godewa gwamnan da karba ta musamman daya musu tareda bayyanawa gwamnan kudirin na TETFUND
Imam yace, dalilin kawo ziyarar jihar borno, domin su duba aikin da kuma duba bukatun sauran jami’un dake cikin jihar.
Gwamna Zulum ya godewa tawagar bisa ziyarar dakuma kaddamar da jami’ar ta kimiya da fasaha a jihar, tareda tabbatar wa da hukumar ta TETFUND cewa gwamnatin sa zatayi aiki hannu da hannu da hukumar domin samun cigaba a kudirin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply