Zaa Farfadowa Da Kamfanin Robobi Ta Borno Plastic A Cewar Gwamna Zulum .

zulum (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Dan gane da farfadowa da kamfanin robobi ta Borno Plastic da Gwamna Babagana umara Zullum yayi a kwannanan hukumar ciyar da harkan noma ta kasa NALDA ta baiwa kanfanin robar kwangila na buga musa manyan buhuhuna milliyan biyu.

Shugaban Hukukmar Prince Paul Ikonne shine ya bayyana hakkan a lokacin da ya jagoranci darectoci zuwa offishin gwamnnan domin ziyarar bangirma.

Ikonne ya bada tabbacin cewa Hukumar NALDA zata cigaba da harkokin kasuwanci da kamfanin ta Borno Plastic domin ciyar da kasuwancin cikin gida gaba.

Ya kuma sanarwa Gwamna zullum cewa sun kawo ziyarrar ne akan umarnin da shugaban kasa ya bayar na farfado da gonakin hukumar a cikin dukkan jihohin kasar.

Bugu da kari Ikonne ya bayyana cewa jihar Borno na daya daga cikin jihohi da aka zaba inda za’a yiwa matasa dubu bitu da arba’in horo tare da basu kayayyakin aiki a bangaren kiwon kifi.
Karkashin shirin tallafawa matasa manoma wanda shugaba Buhari ya kaddamar a watan nowamba cikin shekarrar da ya gabata.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply