Za’a Fara Sarrafa Shara Ana Yin Interlocks A Najeriya

nigeria
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kwamitin zartarwa na shugaban kasa wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ya amince da kafa tsarin da za’a dinga amfani da shara wajen sarrafa wasu abubuwa da samar da ayyuka ga matasa da kuma tsaftace mahalli a kasar.

Ministan muhalli Alhaji Muhammad Mahmood ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasar bayan fitowarsu daga taron a Abuja.

Yace tsarin zai samar da hanyar da za’a dinga sarrafa sharar daga gwamnatin tarayya, jihohi, kananan hukumomi, ma’aikatu, kungiyoyi masu zaman kansu da masu ruwa da tsaki.

Haka nan yace abu ne da za’a hada hannu da karfe wajen gudanar dashi wanda zai kawo tsabtar muhali da samr da ayyukan yi.

San nan ya kara da cewa a yanzu shara nada matukar amfani kuma za’a dinga sake sarrafa ta.

Inda yace a yanzu suna da guri a Karu inda za’a dinga sarrafawa anayin interlocks da sauran abubuwa.

A nata bangaren Ministar walwalar jama’a Hajiya Sadiya Umar-Farouk ta bayana matsalolin da ma’aikatar ta take fuskanta, Inda ta ayyana rashin kudade da rashin matsuguni a matsayin kalubane da ma’aikatar ta take fuskanta.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply