Yarinyar Da Yan Kungiyar Asiri Suka Cire Mata Al’aura Ta Rayu Kuma Tana Samun Kulawa A Asibitin Koyarwa Na Mallam Aminu Kano.

map-of-bauchi-state
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rahoto ya bayyana cewa yarinyar da yan kungiyar asiri suka cire mata al’aura ta rayu kuma tana samun kulawa daga asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano dake jihar Kano.

Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jihar Bauchi DSP Ahmed Mohammed Wakil ya bayyanawa manema labarai cewa an ceci yarinyar kuma an rike ta a asibiti inda take samun kulawa.

Wakilin PR Najeriya mai zaman kansa ya tabbatar da hakan.

Yayin da Haj. Hauwa Inuwa Dutse jami’ar hulda da jama’a na asibitin koyarwa na Aminu Kano take jawabi, tace suna iya kokarin su wajen kulawa da mara lafiyan domin ganin ta koma lafiya kamar da.

Haka kuma rahoto ya nuna cewa gwamnan jihar Bauchi Dr. Bala Muhammad yace gwamnatin jihar zata dauki nauyin yarinyar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply