
Yan ta’adda sun kai hari garin Tumur dake jamhuriyyar Niger Republic wanda yan gudun hijira daga najeriya sama da dubu 40 ke mafaka a wurin.
An kai harin ne a ranar lahadi wanda wasu daga cikin iyalin yan gudun hijirar daga Maiduguri suka bayyana cewa harin yayi muni wanda aka kashe mitane 51 tare da lalata dukiyoyi harma da dabbobi kuma yawancin wadanda suke mafakar sun fito ne daga karamar hukumar Abadam.
A baya irin hakan ya taba faruwa a watan mayun wannan shekara wanda ya tilasta iyalai subu 2 tserewa zuwa garin Damasak don kare rayuwar su.

Haka zalika jami’an gwamnati da kuma kungiyoyin kasashen waje sunce garin na Damasak zaici gaba da fuskantar shigar jama’a daga Niger cikin kwanakin nan
Kuma jami’an sunyi kira ga gwamnati da sauran abokan da ayi tanadin abin bukatu da kuma abincin ga wadanda ake sa ran zasu ison
