Yan Sandan Sun Tabbatar Da Sace Sarkin Bungudu

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna sun tabbatar da sace Sarkin Bungudu, jihar Zamfara, Alhaji Hassan Atto, da adadin wasu da ba a bayyana adadinsu ba, a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, a Kaduna. ya ce a ranar 14 ga Satumba, da misalin karfe 3.10 na yamma, rundunar ‘yan sandan Kaduna ta samu wani mummunan rahoto na farmaki da garkuwa da mutane a kewayen kauyen Dutse da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Ya kuma ce ana zargin mutanen da ba a bayyana adadinsu ba da aka sace, yayin da wasu biyu suka samu munanan raunuka kuma a halin yanzu suna karbar magani. Hakanan, bayanan da aka samu sun nuna cewa an sace Sarkin Bungudu, Jihar Zamfara,

Mai Martaba (HRH) Alhaji Hassan Atto, yana cikin mutanen da aka sace zuwa inda ba a sani ba, ”in ji shi.

Rahotannin da rundunar ta samu sun nuna cewa ‘yan fashin sun tare fasinjojin, inda suka yi ta harbe -harbe ba kakkautawa, kafin su yi garkuwa da wadanda suka kashe.

Ya ce an tura jami’an rundunar don dawo da zaman lafiya a yankin, wanda a sakamakon haka wani jami’i ya rasa ransa . Jalige ya kara da cewa an kwato motoci hudu daga wurin, amma har yanzu ba a san adadin mutanen da aka sace ba.

A halin da ake ciki, an tura tawagar masu ba da taimako zuwa yankin, da nufin ceto wadanda abin ya rutsa da su ba tare da sun ji rauni ba, in ji Jalige.

Dandal Kura Radio International ya tattara rahoto cewa Hassan Attahiru shine babban sarkin masarautar Bungudu a jihar Zamfara.