Yan Sandan Sama Da 500 Da Aka Horas Zasu Fara Aiki A Jihar Katsina.

Nigerian-police-thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sabin Yan sanda dari biyar da hamsin da hudu da aka yaye daga cibiyar horras na yan sanda ta kaduna zasu fara aikin a matsayin yan sandan cikin gida a jihar katsina.

Kwamissinnan yan sanda na jihar Katsina Sanusi Buba,shine ya bayyana hakkan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a headikwatansu.

Ya kuma yi kira ga sabin yan sandanda su kasance masu kwazo da bin dokoki.
Ya kiraye su dasu yi kokari wajen ganin sun rage kannanan laifuka a cikin al’umma tare da bin tsari da aka daura su akai a yayin da ake horas da su.

Buba ya kuma kara da cewa suma zasuyi aiki a matsayin dan sanda mai cikkeken iko kuma zasu sanya inifom baki batare da sun dauki bindigaba.

Gidan Radiyo Dandal Kura Radio International ta bayyana cewa hukumar yan sandan jihar katsina zata samar offishoshi goma domin wanzar da zaman lafiya a cikin jihar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply