Yan sanda sun capke wani mai sana’ar makamai tare da wasu guda hudu a jihar Zamfara

Hukumar yan sanda na jihar Zamfara sun capke wasu hatsababbun yan bindiga, garkuwa da mutane, sace awakai dama kamasu dama mallakar munanan makamai.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Shehu Mohammedya bayyana cewa sakamakon hadin gwiwa da kungiyar makiyaya Fulani na Miyetti Allah ne suka samu nasarar cabko mabarnata jumma’a a Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN).

Yace rundunar yan sandarr jihar a shirye take tayi aiki da kowa domin tabbatar shafe ayyukan barna a jihar Zamfara
Cikin abubuwa da aka gano daga mabaratan a jiya 14 ga watan mayun wannan shekara akwai, bindiga kirar AK-47 guda hudu, harsashai da kayan surkulle

Kuma ana tuhumar abarnata da aikata barna a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina da jihar Niger.

Shehu Ali Kachalla na daya daga cikin wadanda aka capken wanda ya shaida cewa ya debi shekaru sama da uku yana sayar da makamai a yankin arewa maso yammacin kasa sai kuma wani Abubakar Ali da yayi garkuwa da mutane, dama yin kisa tsakanin kananan hukumomin Kagarko da Chikun na jihar Kaduna.