Yan pensho A Jihar Adamawa Sun Fara Addu’o’I Domin Allah Ya Kawo Musu Dauki Sakamakon Bashin Da Suke Bin Gwamnatin.

adamawa-state
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kungiyar yan pansho ta kasa reshen jihar Adamawa kwamred Samson Almuru yace yan pamshon jihar Adamawa sun fara addu’o’I domin Allah ya kawo musu dauki sakamakon bashin da suke bin gwamnati na sama da naira biliyan 2.

Yayin da yake jawabi gay an pansho a sakatariyan kungiyar domin bikin ranar yan pansho ta duniya Kwamred Almuru yace tun bayan hawan gwamnati mai ci mulki a jihar babu wani dan pansho day a karbi dukkan gratutin sa inda yace wasu yan panshon an basu dubu 50 zuwa dubu dari 2 cikin gratutin su.

Haka kuma ya koka da rashin sanya shuwagabannin kungiyar cikin tsarin sabon albashi mafi karanci, inda yace an biya naira dubu 4 ga yan pansho a jihar.
Dokar yan pansho ya bayyana cewa ya kamata a duba kudin panshon lokaci zuwa lokaci domin akwai karuwa a albashin ma’aikata.

A yanzu adadin kudin dayan panshon suke bin gwamnati a jihad a kananan hukumomi baki daya ya kama naira biliyan 20.

Daga karshe ya yabawa gwamnatin jihar da ta sanya sama da yan pansho dubu 3 daga ma’aikatan kananan hukumomi zuwa yan pensho, yace akwai ma’aikata sama da dubu 1 da har yanzu ba a gano sub a.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply