
Hukumar hana bazuwar cututtuka na najeriya tace akalla yan najeriya miliyan daya ne zasu samu alluran sinadarin COVID-19 a watan maris na sheakara 2021 mai kamawa.
Darakta janar na hukumar Chikwe Ihekweazu ne ya bayyana hakan yayin jawabi wa manema labarai. Yace an amince da sinadarin kuma ma Najeriya tasha yakar cututtuka irin su kenda da shan inna ta hanyar amfani da sinadarai.
Kuma yace hukumar NCDC tana nan tana kokarin wayar da kan yan Najeriya game da muhimmancin sinadarin a duk fadin kasar.

Dr Ihekweazu ya kara da cewa daga lokacin da za’a karbo sinadarin cikin farkon shekarar mai kamawa, za’a samu daruruwan jama’a da zasu amfana dashi.
