
Rahotanni na nuna cewa yan kungiyar Boko Haram sun lalata wutar lantarki dake bada wuta a Maiduguri na jihar Borno.
Gidan radio dandal kura ta gano cewa rashin wutar lantarki da ake fama dashi ya zone sakamakon lalatawar da yan Boko Haram sukayi a yankin Mainok dake kan titin Maiduguri zuwa Damaturu.
Rashin wutar lantarkin na tsawon kwanaki ya sanya jama’a da dama koma anfani injin janareto da kuma wutar solar.

A yanzu dai ana kokarin gyara domin samar da wuta ga a garin na Maiduguri.
