Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kashe Matafiya Kuma Sun Kwace Motoci 11 A Jihar Borno.

boko-haram
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Yan kungiyar Boko Haram sun kashe wasu daga cikin matafiya a garin Aligambori dake kusa da garin Gajiram dake kan titin Maiduguri zuwa Monguno a jihar Borno.

Wani wanda ya gani da idonsa ya bayyana cewa lamarin ya faru ranar Laraba inda har yanzu ba’a san iyakar wadanda abun ya shafa ba.

A cewar wani direba mai bin hanyar yace maharan sun kwace motoci 11 daga hannun direbobin sun shiga daji dasu.

Haka nan ya bayyanawa wakilinmu cewa suna yawan saka shingen bincike a garin Aligambori

Wani matafiyi mai suna Abba Monguno ya bayyana cewa a yanzu titin Maiduguri-Monguno ya zama abun tashin hankali inda matafiyan da direbobin duk suke a tsorace yayin ana kai musu hari a kowane lokaci a daya daga cikin shingen bincike guda 4 dake kan hanyar.

Abba ya kara da cewa maharani na yawan aikata harin nasu a shingen bincike inda suke kwacewa mutane kayansu da kudade daga hannun direbobi.
Haka nan yace shingayen binciken guda hudu dake kan hanyar sune wanda ke Tuhuba, Kwanan Tsamiya, Aligambori da kuma Ayikime inda suke tsaida mmatafiiya su kwace musu kaya, wayoyi, kudi harma da kayan dake jikin mutane.

Abba ya kara da cewa duk da rashin kyawun hanyar suna sadaukar da rayukan su kuma hakan ba zai hana su fit aba domin abun bukata.

Da aka tuntubi magana da yawun rundunar yan sandan jihar Borno, DSP Okon Edet ya bayyana cewa a tuntubi rundunar sojojin Najeriya.

Haka kuma an tuntubi mai magana da yawun rundunar operation Lafiya Dole dake barikin Maimalari a Maiduguri kanal Ado Isa ta wayan tarho amma bai ansa kira ba kuma bai ansa sakon way aba da aka tura masa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply