Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kai Hari Garin Pemi Na Karamar Hukumar Chibok

boko-haram
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari garin Pemi na karamar hukumar Chibok inda suka lalata gine gine tare da sace wani malamin addini tare da wata yarinya.

Mataimakin gwamnan jihar Borno Alh. Usman Kadafur wanda ya kai ziyara yankin inda ya jajantawa iyalan wadanda harin ya shafa tare da basu gudumawa.

Mataimakin gwamnan wanda ya samu rakiyar sanatan dake wakiltar mazabar Borno ta kudu sanata Ali Ndume, ya bada gudumawar mota kirar Hilux ga maharba domin aikin sintiri a kauyen da kuma naira miliyan 1 da digo daya ga iyalai 11 na wanda harin ya shafa.

Sanata Ndume ya bayyana cewa yan ta’addan sun lalata hanyar jin dadin jama’a tare da sanya da dama rasa matsugunai a yankin arewa maso gabas.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply